Rundunar Sojojin Najeriya Sun Tarwatsa Sansanin Wasu ‘Yan Boko Haram A Borno
Rundunar sojin saman Najeriya ta ragargaza mayakan ta’addancin Boko Haram masu tarin yawa a Borno.
Rundunar ta samu labarin yadda ‘yan ta’addan ke dafifi cikin dare a wani sansaninsu da ke Tongule.
Hakazalika, Operation Hail Storm 2 ta aiwatar da wasu hare-hare a Bone da Isari B Musa inda wasu ‘yan ta’addan suka sheka lahira.
Samamen da dakarun sojin sama na rundunar Operation Lafiya Dole karkashin Operation Hail Storm 2 suka aiwatar ya cigaba da bada sakamako mai kyau.
Na karshen da ya faru shine ragargaza sansanin mayakan ta’addanci da kuma halaka wasu daga cikin ‘yan Boko Haram da ke Tongule, Bone da Isari B Musa a ranar 24 ga watan Satumban 2020.
Samamen da dakarun suka kai Tongule an kai shi ne sakamakon tabbacin da suka samu na cewa ‘yan ta’addan na zama a yankin da dare kadai Kamar yadda ya dace, jiragen rundunar sojin saman dauke da bindigogin yaki sun kai hari yankin da dare, inda suka halaka da yawa daga cikin ‘yan ta’addan.
A Bone, kusa da yankin Yale-Kumshe, jiragen yakin sun kai samamen bayan tabbataccen bayanin sirri da suka samu.
Jiragen dakarun sojin saman sun sakarwa yankin bama-bamai tare da zuba musu ruwann wuta, lamarin da yasa sansanin da wasu mayakan suka halaka.
Hakazalika, a Isari B Musa, da yawa daga cikin yan ta’addan sun mutu sakamakon harin ba-zata da jiragen yaki suka kai dajin.
Daga Comr Haidar H Hasheem Kano