Mata iyayenmu

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Jihar Kano Ta Kama Mutumin Da Yayiwa Mata 40 Fyade Da Dattijuwa ‘Yar Shekara 80.

Rundunar ‘yan sanda a Kano ta kama wani mutum dan shekara 32 mai suna Muhammad Alfa bisa zargin yiwa wasu mata 40 fyade a shekarar da ta gabata a cikin jihar.

Mai Magana da Yawun Rundunar A Jihar Kano DSP Abdullahi Haruna shine ya tabbatar da kamun a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Kano.

Ya ce wanda ake zargin wanda aka fi sani da suna “Mai Siket” ya dade yana kutsawa cikin gida yana yiwa mata fyade.

Wanda ake zargin ya ketare wani gida a cikin garin Kwanar Dangora, kuma ya shiga dakin yaran, yayin da yake aiwatar da aika-aikar ne mahaifiyar yaran ta kama shi tare da sanar da makwabta.

Wanda ake zargin ya gudu, amma makwabta sun kama shi, kuma sun mika shi ga ‘yan sanda.

Haruna ya ce a yayin bincike wanda ake zargin ya amsa laifin fyade fiye da mata 40 a cikin shekara daya da ta gabata, ya kara da cewa wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun hada da yara da wata mata mai shekara 80.

Ya kara da cewa Rundunar ta fara karbar koke ne daga hannun wadanda lamarin ya shafa din.

Kakakin ya ce Kwamishinan ‘yan sanda Mista Habu Ahmad ya bada umarnin a tura wanda ake zargin zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID) don gudanar da bincike.

A cewarsa, za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu bayan bincike.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button