Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kashe mutane hudu da ake zargi da laifin garkuwa da mutane tare da cafke wasu 13 a wani samame da ta kai a sassan jihar.
Da yake bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargin, mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Manir Hassan, ya shaida wa manema labarai cewa, an kashe wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne a yayin da ake artabu da bindigogi a wurare daban-daban a jihar Kaduna, yayin da aka kama su bisa rahotannin sirri da suka samu kan wadanda ake zargi da ayyukan.
A cewar kakakin ‘yan sandan, daga cikin wadanda ake zargin akwai Auwal Saidu, wani jami’in tsaro mai zaman kansa, wanda ake zargin shi ne ya kitsa sace ubangidan nasa daga gidansa, sannan ya karbi kudi naira miliyan 10 a matsayin kudin fansa kafin shi da ‘yan kungiyarsa su sako wanda aka kashe.
Wasu daga cikin kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da bindigu kirar AK-47 guda 2 da na revolver guda uku da babura biyu da harsashi masu rai 15 da kuma buhunan tabar wiwi.
Kakakin ‘yan sandan ya bayyana cewa za a gurfanar da duk wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincikensu.