Tsaro

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wata Mace shugabar masu garkuwa da mutane a jihar kano.

Spread the love

‘Yan sandan sun cafke mutum 4 wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne bayan sun ceto Wanda akayi garkuwa da shi.

Kungiyar da ake zargin masu satar mutane ne karkashin jagorancin wata mata mai suna Maryam Muhammad da akafi Sani da Hajiya, mai shekaru 23, sunyi aiki a zamfara da Kano kafin a kamasu inji kakakin rundunar ‘yan sandan jihar kano DSP Abdullahi haruna, kamar yadda ya sanar a yau laraba.

Sauran mambobin ‘yan kungiyar da ake zargin sun hada da Sani Ibrahim, mai shekaru 35, wanda akafi Sani da Mailafiya, Shamsudden Sulaiman, mai shekaru 21, dukkan su daga kyauyen butsa karamar hukumar gusau jihar Zamfara.

Sai Ishaq Khalid Wanda akafi Sani da Baban Basma mai shekaru 32 daga Rijiyar Lemo karamar hukumar Fagge dake jihar Kano.

Daga Kabiru Ado Muhd.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button