Tsaro
Rundunar `Yan Sandan Jihar Neja Ta Yabawa Al’ummar Jihar.
Kwamishinan `Yan Sandan jihar neja. Adamu Usman ya Jinjinawa al’ummar Jihar bisa yadda suka gudanar da bukukuwan Babbar Sallah Cikin Lumana.
Mista Usman “Yace an yi sallah cikin Aminci a duk fadin jihar, Yace ya yabawa mutanen Jihar bisa hadin kan da suka baiwa Hukuminsu alokutan Shagulgulan Sallah Inji Shi.
Usaman ya kara da cewa duk kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar Ba’a samu asarar Rai ko dukiya ba a yayin gudanar da Bikin sallar.
Dan Sandan yayi wannan Bayanin ne Jiya Litinin a Helkwatar `Yan Sandan Jihar Dake Minna Babban Birnin Jihar Neja.
Ahmed T. Adam Bagas