Labarai

Ruwan Sama Ya Hallaka Mutane 7 Ya Jawo Hasarar Dukiyoyi a Jahar Neja.

Spread the love

Jaridar The Sun ta rawaito cewar, Kimanin mutane bakwai ne aka tabbatar da mutuwarsu, wasu kuma suka jikkata sakamakon ambaliyar ruwa a yankin Rafin Sanyi na karamar hukumar Suleja ta jihar Neja.

Lamarin wanda ya faru a ranar Jumma’a, ya lalata gine-gine da dama yayin da manoma suka rasa gonaki da dabbobi da dama sakamakon Ibtila’in.

Shugaban Karamar Hukumar Suleja, Abdullahi Maje, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Minna, babban birnin jahar, ya ce ruwan saman ya fara ne da karfe 9:30 na dare lokacin da yawancin mazauna yankin ke bacci.

Ya ce, Mun riga mun ajiye gawawwaki bakwai a babban asibitin Sabon Wuse kuma muna neman wasu da dama da suka bace.

Gidaje da dama sun rushe yayin da bishiyoyi suka fada kan hanyoyi da ababen hawa ke bi a sassa daban-daban na Rafin Sanyi.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya rushe rufin wasu gine-gine da manyan kantuna da kuma ginin jama’a Inji Shi.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button