Rahotanni

Ruwan Saman Da Akayi Yau A Kaduna Ba Fari Bane Ja Ne…

Spread the love

Ayau Da Rane Dai Allah Cikin Nu’imarsa Ya Saukarwa Da Al’ummar Jihar Kaduna Ruwan Sama, Wanda Aka Wuni Anayi.

Sai Dai Kuma Wasu Daga Cikin Jama’a Sun Lura Da Cewa Wannan Ruwan Fa Ba Fari Bane, Ja Ne.

Domin Kuwa Wasu Ma Har Tara Sukayi Domin Su Tabbatar Da Abin Da Idonsu Yagane Musu.

Wani Mazaunin Unguwar Hayin Rigasa Ya Shaidawa Wakilin Mikiya Cewa Tabbas Fa Wannan Ruwan Ja Ne, Domin Kuwa Ya Tari Ruwan Ba Tare Da Kwanon Sama Ya Tabashi Ba Kuma Ya Ga Ja Ne.

Hakanan Wani Mazaunin Unguwar Hayin Danmani Shima Ya Tabbatar Mana Da Hakan, Inda Yace Sai Da Yaduba Sosai Sannan Yatabbatar. Abin Tambaya Anan Shine, Ko Me Yasa Ruwan Yasauka A Launin Ja?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button