Labarai

Saboda Fargabar Kamuwa Da Cutar Corona Gwamnati Ta Sallami Fursunoni 8,713 A Najeriya. Inji Ministan Shari’a Abubakar Malami.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar cewa ta sallami fursunoni 8,713 a fadin kasar, saboda fargabar yaduwar cutar Coronavirus a cikin gidajen kurkukun kasar.

Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya bayyana haka a wani taro a Abuja ranar Talata.

Wanann sanarwa ta zo ne daga hukumomin shari’a na kasar, inda Ministan Shari’a Abubakar ya bayyana a zaman taron kwamitin da shugaban Kasa ya kafa kan Rage cunkoson kurkuku da yi wa fursunoni afuwa, an yi bitar nasarorin da suka samu tun daga lokacin kafa kwamitin shekaru uku da suka gabata ya zuwa yanzu.

Ministan ya ce sakamakon rangadin da suka yi a gidajen kurkuku da jihohi daban-daban, wannan kwamiti ya yanke shawarar sallamar fursunoni 8,713 a cikin jihohi 18 da suka yi rangadi.

A cewarsa kwamitin ya yi la’akari da irin cunkoson da ke akwai a gidajen kurkuku, wanda kuma akwai yiwar fuskantar hadarin yaduwar cutar corona a cikin irin wannan yanayi.

Daga Haidar H Hasheem Kano

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button