Labarai

Saboda saka Hijabi Matasa sun yi ƙoƙari su cinna wa makaranta wuta a jihar Kwara.

Spread the love

Jami’an tsaro sun ceci makarantar Surulere Baptist a Ilorin a ranar Litinin daga wasu maharan da ba a san su ba.

Makarantar kuma tana da coci wanda ke cikin ginin.

Majiyarmu ta labarta mana cewa, ‘yan maharan wadanda ba a san ko su wanene ba sun cinna wa tayoyi wuta suka jefa su a harabar makarantar da misalin karfe 5 na yamma.

Koyaya, jami’an tsaro da ke wurin sun yi hanzarin kashe wutar da zai haifar da babbar illa ga gine-ginen.

Babu wanda aka kama, amma an tsaurara matakan tsaro a makarantun mishan guda goma na Ilorin da gwamnatin jihar ta rufe biyo bayan takaddama kan hijabi tsakanin al’ummomin Musulmi da Kirista a jihar.

Da aka tuntube shi a safiyar ranar Talata, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Mista Okasanmi Ajayi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce kwamishinan ‘yan sanda, Mista Mohammed Lawal Bagega, ya umarci DPO mai kula da yankin, “Ya share dukkan tayoyin da ba a yi amfani da su ba a yankin, kuma a karfafa tsaro.”

Ajayi, wanda ya ce babu wanda aka kama, ya shaida wa Jaridar DAILY POST cewa, ‘yan sanda da ke wurin sun gano tayoyin, sun kashe wutar kuma sun shawo kan lamarin.

Don kauce wa barazanar karya doka da oda, a ranar Litinin ne gwamnati ta ba da umarnin a tsawaita rufe makarantun goma da abin ya shafa.

”Ana sa ran sun ci gaba da karatu a ranar Litinin, amma tsananin tashin hankali kan batun hijabi ya tilasta wa gwamnati ta tsawaita rufewar har abada.

Al’ummar kiristocin sun dage kan cewa ba za a yarda a sanya wata dokar sanya hijabi a makarantunsu ba kuma suna son gwamnati ta mika makarantun ga masu su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button