Labarai

Saboda yarda da kamun ludayin sabon shugaban EFCC Gwamnatin kasar England na kokarin miko tsohuwar ministan man fetur ta Najeriya Diazini Alison Madueke ga gwamnatin Najeriya domin ta kare kanta game da zargin almundahana da kudaden Ƙasa.

Spread the love

Gwamnatin kasar England Na kokarin miko tsohuwar ministan man fetur ta Najeriya Diazini Alison madueke ga gwamnatin Najeriya domin kare kanta domin kare kanta daga zargin da ake mata Na sama da fadi da wasu kudaden ma’aikatar.

Hakan ya biyo bayan amince wa da aikin sabon shugaban hukumar EFCC Abdurrasheed Bawa da hukumomin kasar England sukayi.

Hukumomin na kasar England sun bayyana sabon shugaban hukumar ta EFCC a matsayin wani matashi mai gudanar da duk wani aiki da zaiyi bisa gaskiya da rikon amana.

Hukumomin kasar England sun ce dalilin da yasa tun farko basu amince da miko tsohuwar ministan man fetur din Najeriya izuwa kasar ba saboda basu gamsu da nagartar tsohon shugaban hukumar ta EFCC Ibrahim Magu ba duba ga yadda akaita kai ruwa rana da ‘yan majalisar kasar ta Najeriya wajen tantance shi, wanda har ta Kai ga Gwamnatin Najeriya ta cire shi sakamakon wasu laifuka da aka kama shi dasu.

Amma yanzu hukumomin kasar England sun ce a shirye suke da su miko tsohuwar ministan man fetur din ta Najeriya Diazini Alison Madueke ga Gwamnatin Najeriya don ci gaba da bincike akan laifukan da ake zargin ta dasu, domin suna kyautata zaton wannan sabon shugaban hukumar ta EFCC zaiyi aikin sa bisa adalci.

Daga Kabiru Ado Muhd

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button