Rahotanni

Sabon Labari: Matar Data Kashe ‘Ya’yanta Guda Biyu Ta Hanyar Yi Musu Yankan Rago Labari Ya Fara Canzawa.

Spread the love

Wata kawar Matar nan da ta kashe ‘ya’yanta guda biyu ta hanyar yi musu yankan rago mai suna Hadiza Nuhu tace Matar ita ce
Ya’ daya tilo a wajen mahaifiyarta Aunty Baby Mata ga Ibrahim Haruna.

Ta kashe yaranta guda biyu har lahira ta kuma sassari cousin dinta Wanda yanzu haka yana kwance a Asibiti.

Ta kara da cewa Hauwa’u bata gudu ko ina ba kamar yadda wasu ke yadawa.

Haka kuma babu batun kishi acikin wannan Al’amari, adai bari hukumomi suyi nasu binciken, sannan mu yiwa kan mu addu’ar neman kariya daga fadawa kowanne irin iftila’i na duniya, in ji Hadiza Nuhu.

Hadiza Nuhu tace ranar Juma’ar nan data gabata muna tare da ita, tare da yaran nan guda biyu, ashe bata sani ba tana daf da fadawa wannan iftila’i.

Akwai tarin abubuwa na rudani acikin wannan al’amari, Allah yabayyana koma menene don Alfarmar ma’aiki (s.a.w), cewar Hadiza Nuhu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button