Kimiya Da Fasaha

Sabuwar Fasaha: Shin Ko Ka San Cewa Zaka Iya Amfani Da Layin Wayarka Ba Da Ka Sakashi A Wayar Ba?

Spread the love

Fasahar eSIM (Embedded-Subscriber Identification Modules).

Ga Masu Amfani Da MTN.

Kwana biyu ko uku da suka wuce hukumar kula fannin sadarwa ta kasa wato NCC ta baiwa layin sadarwar MTN damar gwajin fasahar eSIM a Najeriya wanda na tabbatar dayawan mutanen mu basu ankara dashi ba ko kuma ince basu santaba.

Insha Allahu a wannan rubutu zanyi bayanin menene eSIM da kuma yadda ake amfani da ita da alfanunta.

Menene eSIM?
Cikakkiyar ma’anar kalmar eSIM a turance na nufin “Embedded Subcriber Identification Modules” ko kuma a takaice “embedded SIM” fasaha ce ta amfani da layin waya a cikin wayarka/ki ba tare da layin waya na zahiri da muka sani ba “Physical SIM card”, wannan eSIM din yana zuwa acikin waya ma’ana “inbuilt ne ko ince jikin wayar” acikin duk wayar da ke iya daukarsa ko kuma wayar da ke da fasahar.

Tamkar manhaja ne ma’ana application yake amma zaka iya yin duk wani abin da kake gudanarwa da layin ka na zahiri ba tare da wani matsala ba.

Wannan fasahar dai anfara gabatar da itane a shekarar 2016 kuma tuni kamfanonin waya da kasashe sun fara amfani da wannan fasahar ta eSIM, sai dai mu anan Najeriya sai yanzu ne hukumar sadarwa ta baiwa kamfanin layin sadarwa na MTN damar gwajin wannan fasahar.

MTN zatayi gwajin wannan fasahar har shekara daya kuma duk wanda yake da wayar dake dauke da fasahar zai iya cin moriyar wannan fasahar cikin sauki.

Menene Amfanin wannan eSIM din?

 1. Za’a iya amfani da lambar waya sama da daya a wayar ba tare da SIM card ba na zahiri, misali idan anaso ace lambar wayar mutun na gida daban na kasuwanci daban wannan zaiyu cikin sauki da fasahar eSIM.
 2. Baka/kya bukatar damuwa jirewa ko faduwar SIM domin wannan a jikin wayar yake.
 3. Ana iya canza operator (kamfanin sadarwa) ba tare neman layin kamfanin layi ba, misali da fasahar eSIM za’a iya amfani da MTN, AIRTEL, ETISALAT ko Glo duka a cikin wayar ba tare da an nemo layukansu ba, wannan zai taimaka ga mai yawan bula guro ko da anje inda babu daya layin babu bukatar sai an nemo layin kawai za’a kara ne akan layin da ake dashi ada. ma’ana dai yau in kacanza shawarar baka/kya son amfani da MTN take za’a iya tsallakawa wasu layukan.

Wadannan sune kadan daga cikin amfanin layin eSIM.

Shin Tayaya Zanci Moriyar eSIM na MTN?
A yanzu dai a duka kamfanonin sadarwa da muke dashi a Najeriya kamfanin MTN ce kadai take da damar gwajin wannan fasahar sai dai ba kowane waya bane ke da halin cin moriyar wannan fasahar, dan haka ga duk mai daya daga cikin wayoyin nan kuma nada bukatar gwada fasahar zai iya garzayawa zuwa dukkan MTN office dake kusa dashi, ga wayoyin kamar haka:-

 1. Google Pixel 3, Pixel 3 XL.
 2. Google Pixel 4, Pixel 4 XL.
 3. iPhone 11, iPhone 11 Pro, iPhone 11 Pro Max.
 4. iPhone XS, iPhone XS Max, iPhone XR.
 5. Samsung S20 Series.

Wasu Tambayoyi Da Kila Mai Karatu Zaiyi.

Q: Tayaya Zan daura sannan nayi amfani da eSIM?
A: Domin daurawa tare da amfani da eSIM ana bukatar ziyartar ofishin MTN mafi kusa anan za’a baiwa mutun QR Code da zaiyi scanning a wanann wayar da keson amfani da eSIM sannan ya sauke (downloading) profile dinsa/ta.

Q: Shin zan iya amfani da eSIM profile dina sau sama da daya ko kuma wayoyi biyu?
A: A’a kowane waya zai dau profile dinsa guda ne dan matukar ana son ayi amfani da profile din eSIM a wata wayar daban ba wacca akayi activating da farko ba dole sai ansauke profile din akan wancan ta farkon kan a daurawa wannan din.

Q: Inada wayar da ke iya daukar eSIM tayaya zan samu PUK da Serial Number na SIM?
A: Bayan anyi scanning din QR Code da nafada a farko za’a baiwa mutun slip ko ince sabon SIM PACK dake dauke dukkan wani abu game da eSIM din kamar SIM din zahiri a jiki za’a rububuta PUK, Serial Number da sauransu.

Q: Shin Ina bukatar data dan na sauke profile dina na eSIM?
A: Eh, bayan anyi scanning na QR Code din dole ana bukatar sauke profile dan haka saida damar shiga yanar gida wato (Intenet Connection)

Q: Me zai faru idan na jefar ko kuma wani abu yafaru da QR code dina?
A: Ana iya ziyartar ofishin MTN mafi kusa a kowane lokaci domin sake karban QR code, kawai dai za’abi hanyoyin tabbatar musu eh eSIM din naka/ki ne.

Q: Nagwada sauke eSIM profile dina/ta amma yaki?
A: Idan aka fuskanci wannan matsalar a duba daya daga cikin hayoyin nan

 1. A fara dubawa ko anriga an sauke profile din akan wayar (Zai iya hanashi sake downloading).
 2. A duba ko anriga anyi activating eSIM din akan wayar.
 3. A tabbatar wayar nada damar shiga yanar gizo (Intenet Connection)
  Q: Shin sai na biya wani abu kan a daura mun eSIM?
  A: Kamfanin sadarwa MTN tace daura eSIM kyauta ne.

Q: Shin tayaya zan canza eSIM dina daga wannan wayar zuwa wancan wato (eSIM swap)?
A: Hanyoyin duk daya suke da SIM swap na zahiri kawai ana bukatar sake downloading din eSIM profile dinne akan wanan sabon wayar da akeso a daura.

Q: Shin zanyi rejistan eSIM dina ne?
A: Eh, dole sai anyi rejista kuma hanyoyin rajistan duk daya yake da SIM na zahiri da muke amfani dashi yanzu kuma da zaran an kammala za’a baiwa mutun SIM PACK mai dauke PUK da lambar nasa (sabon lamba ne matukar swapping akaiba).

Q: Shin ina iya maida lambar layina na zahiri yakoma lambar eSIM?
A: Eh ana iya maidawa kawai aje ofishin MTN mafi kusa.

Q: Shin bayan na canza lambar layina na zahiri yakoma eSIM zan iya dawowa dashi?
A: Ana iya dawowa dashi kuma duka hanyar dayane da SIM Swap.

Q: Tayaya zan tabbatar eSIM yahau kan wayana?
A: Da zaran yahau za’a ga alamar yahau a saman wayar.

Q: Wace hanya zanbi dan nadaura eSIM profile dina kan iPhone dina ko Google Pixel?
A: Ga na iPhone:

 • Da farko a tabbatar an karbo QR code din a ofishin MTN sai aje
 • Settings > Cellular > add a cellular plan
 • Sai ayi scanning QR code din saura a karasar a ofishin
  A: Ga na Google Pixel 3:
 • A shiga settings sai aje “Network & Intenet”
 • A zabi “Mobile Network”
 • Adanna “Advanced” sai a zabi “Carrier” sai a sake zaban “Add Carrier”.
 • Sai ayi scanning din QR code din
  Shikenan Mai tambaya zai iyayi.

Muhammad Baba Goni (Royalmaster).

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button