Sakamakon Karya Ake Yadawa Wai PDP Ce A Gaba, Inji APC.
Yau 19, Satumba 2020, rana ce mai da mutanen sukayi amfani da amfani da ita ta hanyar zaben dan takarar da suka fi so.
Kamar yadda kowa ya sani akwai ‘yan takara da yawa da ke takarar kujerar mafi daraja ta daya a jihar.
Hakanan jefa kuri’a ya kare a mafi yawan rumfunan, kuma sakamakon yana ci gaba da gudana kamar yadda shugabannin rumfunan zaben suka sanar.
Haka zalika, jam’iyyar All Progressives Congress APC mai mulki a Abuja, a cikin wata sanarwa da kakakin kwamitin yakin neman zaben ta (ya yi dariya kan sakamakon da yace PDP ta kirkira, inda suka rinka fitar da alkaluman karya ta hanyar nuna cewa ta riga ta samu kuri’u mafi rinjaye).
A cewar sanarwar, PDP ba za ta amintar da su zaben ba, lura da cewa alkalumman da hotunan da ake yadawa a kafafen yada labarai karya ne, bai kamata a dauke su da mahimmanci ba.
Jaridar Vanguard ta rawaito cewa am’iyyar ta APC ta kara ba jama’a shawara da su yi hankali da irin wannan karyar da sakamakon zaben Jihar Edo da ke gudana a kafafen sada zumunta.
A halin da ake ciki, Jam’iyyar PDP, ta sanar cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC, da Sashin Hidimomin Jiha, DSS, suna yunkurin sauya sakamakon zaben inda PDP ke kan gaba, musamman a Yankin Sanatan Edo ta Arewa.
Zargin na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakinta, Kola Ologbondiyan. Hakanan jaridar Vanguard ta ruwaito.