Labarai

Sako Zuwa ga Mutun Dari da Sanata Uba sani ya dauki nauyi domin Samun Milyan Bibiyu Zuwa Milyan uku uku…

Spread the love

Ana sanar da mutun dari wa’yanda aka koyar dasu dabarun kiwon kifi da kiwon kaji wanda Cibiyar Uba sani, Uba Sani Foundation, kungiyar agaji da tallafawa suka koyar, ana sanar da mutun darin 100 wadanda suka amfana da horon aikin cewa su Kula zasu karbi sakon SMS daga Bankin NIRSAL Microfinance Bank dauke da hanyar haɗin alkaluman yanar gizo Links) wanda ake so su shiga su danna (Click) don karɓar tayin amincewa da rancen kuɗaɗen hannun jarin na Agri-Business Small and Medium Enterprises Investment (AGSMEIS), don kafa kasuwancin su Wanda Kuma bayan sun sami horo kuma suna jiran ƙarin umarnin.

Fitaccen sanata Uba Sani wanda bai Gaza cika alkawuransa ba ta wannan yunkurin ya sake sanya himma a zukatan wadanda suka sami horon kuma suka jira alkawarin da ya yi na hada su da tallafin kudin don dogaro da kai. Ya bukaci masu karbar kudin da su kammala bayanan sirrin da ake bukata bisa ka’ida kuma su bi a hankali don kaucewa kurakuran da ka iya kawo tsaiko ga biyan su kudin har’ila yau Fitaccen sanata Uba Sani ya sake aikewa da sakonnin fatan alheri zuwa ga mutanen kirkin da yake wakilta na mazabarsa tare da rokon su da su ci gaba da tallafawa manufofin kyakkyawan shugabanci na amintaccen Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El Rufa’i…

Sanarwa daga Abubakar Rabiu Abubakar, Babban jami’in yanki na mazabar dan majalisar dattijai kaduna ta tsakiya. Yau 10 ga watan satumba, 2020

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button