Labarai

Salihu Tanko Yakasai Da’ala dai bai dakatu ba domin kuwa ya cigaba da aikinsa kamar yadda ya saba.

Spread the love

Dukda cewa An dakatar dashi Har’ila yau Salihu Tanko Yakasai ya cigaba da aikinsa kamar yadda ya saba domin kuwa yau an hangoshi ya fitar da labari yana mai cewa Mai girma Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje (OFR) ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa na wannan makon wanda a ka gudanar da shi a dakin taro na Africa House da ke fadar gwamnatin jiha a Kano.

Taron zaman majalisar ya samu halartar Mataimakin Gwamna Dr Nasiru Yusuf Gawuna da Sakataren Gwamnati Alhaji Usman Alhaji da Shugabar Ma’aikata ta jihar Kano Hajiya Binta Lawan Ahmed da Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati Ali Haruna Makoda da Kwamishinoni da sauran yan Majalisar. sai dai wannan sanarwar tasha ban ban dana yadda yake fitar wa a baya domin kuwa a karshen sanarwar an hango ya rubuta kamar haka Abba Anwar
Babban Sakataren Yada Labaran Gwamna
Laraba, 14 ga Watan Oktoba, 2020

a maimakon sunansa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button