Labarai

Sama Da Almajirai 30 Ne Suka Gudu A Gurin Da Aka Killace Su A Jigawa.

Spread the love

Daga Haidar H Hasheem Kano

Wannan lamarin yafarune a jiya Litinin inda almajiran da gwamnatin jahar Jigawa take killace dasu bayan dawowa dasu da gwamnatin Kano tayi zuwa jahar ta Jigawa.

Majiyarmu ta shaida mana cewa almajiran sun kai adadin mutum Dari biyar, wanda aka killacesu a sansanin yan bautar kasa dake karamar hukumar Kiyawa a jahar ta Jigawa.

Hukumar kula da cutar Corona Virus ta jahar jigawar ta shaidawa Channel Tv a jiya litinin din inda ta tabbatar da faruwar lamarin.

Amma gwamnatin jahar Jigawa tace wadanda suka tsere daga wajan da aka killacesu din ta samu damar cafkosu kuma tadawo dasu dukkansu baki daya.

Amma gwamnatin ta ce iyaye suna taka muhimmiyar rawa kan harkar almajirta a sassan kasar nan baki daya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button