Labarai
Sama da mutane miliyan 2 ne suka rasa Mazauninsu sakamakon ta’addanci a Najeriya – FG
Sama da mutane miliyan 2 sun kasance ƴan gudun Hijira ta dole Sakamakon hare-haren ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane a Najeriya.
Ministar jinƙai da kuma tallafawa ƴan gudun Hijira Sadiya Umar farouq itace ta bayyana hakan sannan ta yabawa shugaba Muhammadu Buhari kan goyon
Baya domin ganin a tallafawa ƴan gudun Hijiran.
Idan zamu tuna tun daga shekarar 2009 zuwa yanzu Kasar Nijeriya tana fama da rashin zaman lafiya da rikice-rikicen addini da ƴan tada ƙayar baya suke haddasa wa a faɗin Kasar. Daga El-farouq jakada