Samun Zaman lafiya shine mafi komai ga Rayuwar Bil’adama ~Aisha Buhari
Uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Muhammadu Buhari, ta bukaci matan gwamnonin jihohi da su taka rawa wajen gina zaman lafiya da hana rikice-rikice a jihohinsu.
Misis Buhari ta umarci matan gwamnonin da su tattara kan su tare da jawo hankalin mata da matasa don wannan gagarumin aiki, wanda ke da muhimmanci ga rayuwar dimokuradiyya.
Wata sanarwa daga mai taimaka wa shugabar na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kai na ofishin uwargidan shugaban kasar, Aliyu Abdullahi, ya ce Mrs Buhari ta yi magana ne a yayin wani taron karawa juna sani kan wayar da kan mata da matasa don samar da zaman lafiya, sulhunta rikice-rikicen al’umma da kuma juriya a cikin bayan COVID- 19 a ƙarshen mako.
Matar shugaban kasar, wacce Dakta Hajo Sani, babbar mataimakiya ta musamman ga shugaban kasa kan harkokin mulki da harkokin mata Wacce ta wakilci Shugaban Buhari ta lura cewa annobar COVID-19 ta haifar da rikicin duniya kamar yadda aka nuna a cikin fushi, zanga-zanga a duk duniya. kazalika da tashe-tashen hankula, wanda akasarin wadanda abin ya shafa mata ne da matasa.
Misis Buhari ta ci gaba da lura cewa matasa da mata na cikin matukar damuwa ga rikice-rikicen annobar kamar yadda yawancin su yanzu ke cikin kasadar barin su a baya a fannin ilimi, damar tattalin arziki, da kiwon lafiya da walwala a yayin wani muhimmin mataki na rayuwarsu.
“Don haka, ya zama wajibi mu himmatu wajen wayar da kan mata da matasa don samar da zaman lafiya, warware rikice-rikicen al’umma da juriya. Wannan ya fi dacewa a kan wadanda ke kan mukamai kamar matan shugaban kasa, ”inji ta.