Sana'o'i

Sana’a: – Sana’a Itace Take Yanke Talauci Ta Samar Maka Da Matar Aure.

Spread the love

-Sana’a tana yanke talauci.
-Sana’a tana Samar da Matar Aure.
-Sana’a tana kulla Zumunci.
-Sana’a tana ƙara daukaka.
-Sana’a tana ƙara fahimta.
-Sana’a tana karfafa Dangantanka
tsakanin Mutum da mutum ko Gari Da Gari.

Kaɗan daga cikin Alfanun Sana’a kenan, duk a sanadin ta zaka iya Mallakar waɗan nan abubuwa, har ma fiye da haka, matuƙar ka gina ta akan tafarkin Gaskiya taimako da fidda Hakkin Allah.

Akwai Sana’a kala kala wasu da manya jari wasu da kananun Jari, Amma duk sunan su Sana’a ne, Koda Naira dubu daya 1,000 zaka iya farawa harma ƙasa da haka, domin akwai ƙananun sana’o’i wanda jarin su ma ba ya kaiwa haka, kuma da hakan wasu sukeci suke sha.

Karka Raina Sana’a komin ƙanƙantar ta, Domin Da Zakaje ka tambayi manyan ‘yan kasuwa Zakaji Cewa, suma da ƙananun Sana’a kuma ƙaramin jari suka fara kafin sukai ga matakin da suke ciki A yanzu.

Shin me kuke jira baku fara sana’a ba?

Duk Gatanka, tashi ka nemi na kanka Domin Shine kake da iko da kuma alfahari dashi!!!

Sannan Ban Yarda Cewa Babu Aikin yi ba,
Amma Na Yarda Cewa Mune Muka Girmi Aikin Daya dace Damu.

Mecece Sana’ar Gidan Ku?

Je ka Ka Bincika, Na San Ba za arasa ba.

Domin Babu Mutanen Da basa Zama ba Sana’a Koda kuwa Noma Ne!!!

Daku Nake ‘yan uwana Matasa.

Kowa ya zauna zai ga Zaunau.

Allah yasa mudace Amin

Daga Hussaini Abba Dambam, Karamar Hukumar Dambam Jihar Bauchi Najeriyar 08140501505
08020814173

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button