Ƙwacen waya: Wani matashi ya shiga gidan matar aure ya caccaka mata sukun direba


Shidai matashin da ake zargi, ya addabi gidajen jaoji dake Kano da jerin sace sace ne.

To amma, kamar yadda ake cewa ne, rana dubu ta barawo amma guda ɗaya tak ta mai kaya ce.
Hakan kuwa akayi, domin cikin ikon Allah, Sa’a ta ƙare masa ne, yayin da aka cafke shi hannu dumu-dumu yana hakilon daɓawa wata matar aure sukun direba, duk a ƙoƙarin da yake na yaga ya rabata da wayar salular ta.


Radiyo Freedom dake jihar Kano ta rawaito cewar, matashin dan unguwar Sheƙa ne, kuma sunansa Muhammad Isah, wanda akewa laƙabi da “Gunki”.
Da yake bayyanawa Freedom radiyo abinda ya faru, mai sukun direba, ya bayyana ya akayi ya shiga gidan har kuma ya caccaka mata sukundireba. Ga abinda yace:

“Gaskiya nine na caka mata sukundireba kuma nayi hakan ne da nufin na kwace mata waya, amma nayi nadamar wannan ta’addanci da nayi” a cewar Muhammad Isah.


Itama matar da tace kada a faɗi sunanta saboda gudun yamaɗiɗi, cewa tayi, kawai tana cikin ɗaki, sai taga mutum akanta, koda taga haka, sai ta zata ɗanta ne.


Amma daga baya, sai ta fuskanci ai bashi bane, ai kuwa nan da nan sai ta cakume ƙafarsa, hakan da tayi, tasa baiyi wata wata ba ya zaro sukundireba yasoma caccaka mata.


Faruwar abin ya gigita mutanen unguwar sosai, wanda hakan yasa sukace, ya kamata hukumomin da abin ya shafa dasu ƙara ƙarfafa matakan tsaro a yankin dama al’umma gabaki ɗaya, duk domin rage ayyukan bata gari kwata kwata.


Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *