Batun Boko Haram: Sanatoci sun razana sosai, abisa cewar ko wani lokaci za’a iya musu hari.

Akwai wani rahoto da yake nuna cewa, ƴan ta’adda sun shirya tsaf domin kai wani gagarumin hari a cikin majalisar dattijai, wuraren da gwamnati ke gabatar da aiyuka, da dai sauran wurare da suke da muhimmanci.

Hakan yasa tuni jami’an tsaro suka tsinkayi wuraren da bincike gamida shawartar mazauna wajen wanda ya haɗa harda da ƴan majalisar akan su kula su sauya yanayin yanda suke gudanar da al’amuran su, ciki kuwa harda canja ƙofar shiga majalisar.

Wannan sanarwar da akayi musu, ta cewa Bokoharam ka iya kawo hari a kowani lokaci, ba ƙaramin gigita ƴan majalisar yayi ba, inda tuni suka canja yanayin salon gudanar da al’amuran su kamar yadda aka buƙata.

Jaridar “The Punch” ta rawaito cewa, ƴan majalisar wakilan ta Najeriya, sun sanar da cewa, haƙiƙa sun samu wannan gargaɗi daga hukumomin tsaro akan yiwuwar kai musu harim tun a ranar laraba data gabata.

Wani ɗan majalisa daya fito daga yankin Kudu maso yamma, ya tabbatar da cewa, daga wannan ranar daya sami wannan sanarwa zai takaita zuwa majalisar.”Akwai maganar tsaro da aka yi mana yau.

Na shirya barin nan. Zan dinga zuwa ne idan manyan abubuwa sun taso kuma an bukaci zuwa na.

Babu inda mutum zai tsira a kasar nan,” yace. Sanarwan an tura ta ne ga kakakin majalisar dattawa, Femi Gbajabiamila da sauran sauran jiga-jigan majalisar da sauran mambobi.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *