Namiji yayi asham a cikin mata sanye da hijabi, amma yazo hannu.

I

Kungiyar yan sintiri da saka kai tayi nasarar cafke wani zabgegen gardi sanye da hijabi goɗoɗo dashi a cikin mata sanda akeyin sallar asham a wani masallaci dake can unguwa uku layin ƴan awaki.

To amma garjejen gardin, yabar baya da ƙura, domin wata matashiya da itama taje sallar, kuma yayi sahu da ita, ta duba sama ko ƙasa bata ga wayar taba, hakan ne yasa ta soma zargin wannan garjejen gardin mai sanye da hijabi.

Shi kuwa matashin daya ɗauki wayar, ai sai ya samfe, ya fice waje abinsa, inda ya tafi bayan bandaki domin cire kayan matan. Ai kuwa, cikin rashin sa’a, yan sintirin suka kama shi.

Koda aka tambayi mai wayar game da wannan gardin, cewa tayi:

“Har muka rabu da matashin, tunanina ƴar uwata ce mace”. Matashiyar ta faɗa.

Adamu Abubakar Fiya Fiya, shine shugaban yan sintiri na yankin ya shaidawa majiyarmu cewa:

“Akwai buƙatar ƴan agajin mu a masallatai su ƙara zage damtse yayi gudanar da tahajjud”.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *