Tashin Hankali yayin da wani mutum ya afka rijiya a jihar Kano, ko yaya aka haihu a ragaya?

A ranar asabar din nan ne wani bawan Allah mai suna Hamisu Ahmed ya afka rijiya a unguwar Samegu bayan Sahad store dake jihar Kano.

Hukumar dillacin labarai ta ƙasa wato NAN, ta ruwaito cewa jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobara, Saminu Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace mamacin wani bakanike ne, wanda ya tafi domin ɗauki wanka , bayan ya tashi daga gyara mota kamar yadda ya saba.

Ya ƙara da cewa, da misalin ƙarfe 07:31 na safe ne, hukumar su ta samu kiran gaggawa daga wani mai suna Muhammad Abdulmalik.

A cewarsa: “Muna samun kiran ne, muka maza muka tura ma’aikatan mu masu ceto wajen a daidai 07:43 na safen,” Inji shi.

Abdullahi ya ƙara da cewa, an ciro Hamisu daga cikin rikitarwa ne a mace, domin ya riga da yace ga garinku nan tun tuni, saboda haka ne aka damƙa gasar tasa a hannun mahaifin mamacin, mai suna Alhaji Yahaya Usman dake Kwatas din Dorayi Chiranchi.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *