Yajin Aikin Kaduna: Yaɗau sabon salo, sakamakon sanarwar da El-rufai ya bayar na neman shugaban hukumar ƙwadago ta ƙasa, Ayuba Wabba.

El-rufai

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-rufai ya sanar da batun neman Shugaban hukumar ƙwadago ta ƙasa, wato “Ayuba Wabba” ruwa a jallo.

Hakan ya biyo bayan zargin da Gwamnatin jihar takewa shugabancin kungiyar wajen jagorantar tsaida harkokin tattalin arziki na jihar, lalata kayan gwamnati datayi domin al’umma da dai sauransu laifuka.

A ranar talata ne 18 ga watan Mayu El-rufai ya sanar da wannan saƙon ta shafinsa na Twitter, inda ya bayyana cewa:


” Duk wanda yasan inda Wabba yake ɓuya yanzu haka, ya hanzarta sanar da ma’aikatar Shari’a ta jihar Kaduna”

Gwamnan ya ƙara da cewa, da akwai lada mai tsoka ga wanda ya samu damar fesar da inda Wabba yake.

Idan za’a iya tunawa, ranar talata 17 ga wata, anga matafiya da yawa sunyi cirko cirko a hanya da tashoshi sakamakon yajin aikin.

Abinda yasa masu siyan tikiti cikin halin tsaka mai wuya, inda aka bayyana musu cewar zasu iya jira a ranar koda wani lokaci ne batare da tikitin su ya lalace ba. Yajin aikin da ba’a janye ba kenan har yau.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *