Labarai

Sanata Ali Ndume, ya bukaci Shugaba Buhari ya Sauya Ministocinsa domin Suna Hana Ruwa Gudu.

Sanata mai Wakiltar Kudancin Borno a majalisar Dattawa, Sanata Muhammad Ali Ndume, Kuma Shugaban Kwamitin Sojoji a Majalisar Dattawa, ya Bukaci Shugaba Buhari ya Rushe Majalisar Zartaswar Kasar Nan.

Ndume, ya yiwa ‘yan jaridu wannan Bayanin ne a Gidansa Dake Maiduguri, a Jihar Borno.

Ndume, yace “Shugaba Buhari mutum ne mai Kishi kasa amma Ministocinsa suke Hana Ruwa Gudu.”

Abin ban Sha’awa a Gwamnatinsa Yadda Akayi Kasafi mafi Yawa a Tarihin Kasar Nan.

Abin Takaici, Yadda Arewa ta zama koma baya a wannan Gwamnatin, kuma laifin Ministoci ne.

“Yace a dai dai lokacin da kasar nan ke fama da matsalar tsaro, musamman Arewa maso Gabas, kamata yayi ministoci su rinka Taimakawa Buhari wajen kawar da Ta’addanci a Kasar Nan.

Ndume, Ya bukaci Gwamnati ta Samarwa Sojoji Wadatattun Kayan Aiki na Zamani domin Kawar da Ta’addancin Boko Haram a Arewa maso gabashin Kasar Nan.”

Ko a Cikin makon da ya gabata Sai da wata kungiyar Dattawan Arewa suka yi barazanar Kai Karar Shugaba Buhari Kotu kan kin Amincewa da yayi ya Sallami Shuwagabannin Tsaron Kasar Nan, Tunda sun kasa kawo karshen ta’addanci a kasar duk da Makudan kudin da gwamnati tace tana basu domin kawar da ta’addanci a Arewacin Kasar Inji Su.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button