Siyasa

Sanata Orji Kalu Na Jahar Abia Wanda Aka Yiwa Daurin Shekaru 12 Ya Koma Bakin Aiki Yau.

Spread the love

Daga Ahmed T. Adam Bagas

A Yau Talata ne dai Tsohon Gwamnan Abia kuma Sanata mai wakiltar Arewacin Abia Sanata Orji Kalu Ya Halarci zaman majalisa.

Sanata Kali dai Wata Kotu a Abuja ta Karkashin Mai Shara’a Muhammad Idris ta Daureshi Na Tsawon Shekaru 12 Kan zarginsa da almundahana da Kudin Jahar har Naira Biliyan 7.65.

An yankewa Kalu Hukuncin gidan kaso din ne Ranar 05 Disamban 2019 Inda Aka tsare shi a Gidan yarin Kuje dake Birnin Tarayya.

Wasu Alkalai ne dai sukayi nazari Inda Suka CE Alkali Muhammad Idris din bai da Hurumin yankewa Kalu Hukunci Daga nan ne Suka bada Umarnin Asaki Orji Kalu ya koma bakin Aiki.

Ranar laraba da tagaba ne aka Fito dashi daga gidan Yarin Kujen Yau Talata kuma ya halarci Majalisa, ya sanarwa yan jarida cewa zai samarwa Al’ummarsa Duk kan abubuwan more rayuwa da Suke Bukata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button