Labarai

Sanata Uba Sani shi daya tal yayi sanadiyyar samuwar Jarin Milyoyin naira ga ‘yan Nageriya sama da mutun Milyan daya a duk fadin Nageriya…

Spread the love

Sanata uba Sani Mai wakiltar kaduna ta tsakiya a Majalisar dattijan Nageriya amatsayinsa na Shugaban kwamitin bankuna Inshora da sauran harkokin kudi yayi anfani da damar da Allah ya bashi ya taimaki Al’ummar Nageriya Baki daya
ta Hanyar Samar da jarin sana’o’i ga matasa sama da mutun Milyan Daya 1m Sanata uba sani shine ya Shiga ya fita yayi aiki ba dare ba rana domin ganin an Samar da kudin Rance daga babban bankin Nageriya Central Bank Of Nigeria CBN, Sanata Uba Sani Sun zauna Sun Shirya shirye shirye na musamman kala kala a Ma’aikatu daban-daban domin tabbatar da Isar da kudaden sana’a ga ‘yan Nageriya musamman matasa, Babban bankin Nageriya CBN ya Aminta da bukatun Sanata Uba Sani Hakan yasa ta Hanyar bankin NIRSAL Microfinance Bank (NMFB) Wanda mallakin Babban bankin Nageriya ne, Bincike ya nuna cewa kawo yanzu sama da mutun Milyan Daya ne Suka anfana da tsarin NIRSAL a shirye shiryen daya ke aiwatarwa na bawa ‘yan Nageriya kudaden kasuwanci domin kawo karshen Zaman Banza da tashe tashen hankula a sassan Nageriya.

Idan baku manta ba Majalisar Zartarwa ta Tarayyar Nageriya a ranar 22 ga Yuli, 2020 ta amince da kashe naira Bilyan N75, 000,000,000.00 (Naira biliyan saba’in da biyar) domin kafa Asusun Zuba Jari ga Matasan Najeriya a shirinta Mai taken 2020 – 2023 Wanda Gwamnatin ta sadaukar duk domin zuba jari ga sabbin dabaru, dabarun Kuma ga hazikan Matasan Najeriya.

Misali Ai Kun San adadin yawan ‘yan Nageriya a yanzu ya Kai sama da mutun Milyan dari Biyu 211,400,708 Kuma kusan mutun milyan dari 100,000,000 suna fama da talauci.

A Shirin Gwamnatin tarayya Mai taken NYIF Wanda aka shiryashi da niyyar tallafawa matasan Najeriya da kudi don samar da akalla ayyuka dubu dari Biyar 500,000 tsakanin Shekara 2020 zuwa 2023. Misalin Yanzu idan akace Jama’ar da suka amfana da tallafin jarin sun Kai mutun milyan daya ya kuke gani idan Ma’aikatu dubu dari Biyar Suka inganta? Shin adadin mutun nawa ne zasu samu aikinyi a karkashin Ma’aikatun?

Har’ila Yau misalin dai, mu dauka ace kana da karamar Ma’aikata Company) sai ka samu tallafin kudi Milyan Goma 10m daga Gwamnati domin ka inganta Ma’aikatarka to Hakan zai baka damar daukar Sabbin Ma’aikata misali ace an Samar da Ma’aikatu Milyan Daya cikinsu ko wacce Ma’aikata ace ta dauki Ma’aikata mutun goma goma 10, kenan mutun Milyan Goma sun Samu Aikinyi daga Ma’aikatu Milyan Daya…

Nasan Kuna sane da Cewa a Nageriya Muna da yawan sanatoci a Majalisar dattijan ta Nageriya har guda dari da tara 109 Hadi da Abuja Mai guda daya shin ya kuke gani idan ace duk sanatocinmu zasuyi aikin basira irin na Sanata Uba sani domin kirkiro hanyoyin da za’a magance talauci?

Wannan fa Sanata daya ne kacal Cikin dari da tara ya Samar da Wannan Hikimar domin Al’umma to Ina ga ace sauran zasuyi irin wannan Aikin alkhari haka, Ni dai a nawa ra’ayin sai nake ganin idan akayi Haka Lallai za’a kawo karshen ta’addanci talauci jahilci da Rashin abinci a Nageriya…

Malam Uba Sani ‘yan Nageriya suna godiya Allah ya saka da alkhari, marubucin shine M Inuwa MH…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button