Labarai

Sanata Uba Sani Ya aika da sakon Ranar Tsarkin kirsimeti ga kiristocin kaduna…

Spread the love

A wata sanarwar daya fitar Sanata Uba Sani Mai wakiltar kaduna ta tsakiya A Majalisar dattijan Nageriya Yace a wannan lokaci na musamman na bikin Kirsimeti, ina Mai aikawa da gaisuwa ta musamman ga ’yan uwanmu Kiristoci maza da mata a Nijeriya da ma duk duniya.
Mun kasance Muna farin ciki tare da ku kuma muna roƙon Allah Maɗaukaki ya kiyaye ku kuma ya ƙarfafa ku yayin da kuke fuskantar ƙalubale da matsalolin da annobar COVID-19 ke haddasawa.

Hutun da aka saba yinsa cikin manyan bukukuwa na Kirsimeti na iya kin kasancewa a wannan lokaci Sakamakon ƙalubalen tattalin arziki,
Dukda Haka Bai kamata mu yi kasa a gwiwa ba wajen yin amfani da damar da take bayarwa don sabuntawar ruhaniya da kuma gina ruhun kadaitaka da jituwa. Haihuwar Yesu Mai tsarki abu ne mai muhimmanci. Niyar Aikinsa ta kasance mafi mahimmanci da tasiri. Ya yi wa’azi da soyayya, gafara, adalci, tawali’u, aminci da sadaka. Ya tsaya tsayin daka domin talakawa, raunana.

Ina roƙonmu da mu yi amfani da lokacin Kirsimeti domin sanya murmushi a fuskokin talakawa da masu raunin cikinmu. Lallai zamani yana da matukar wahala. Amma dole ne mu ciro daga halinmu na alheri don kula da waɗanda ba su da ƙarfi. A matsayinmu na shugabanni dole ne mu tsara tare da aiwatar da shirye-shiryen saka jari na zamantakewar cigaba don rage tashe tashen hankali a ƙasarmu. Inji Sanatan.

Haka Kuma sanatan ya Kara da Cewa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta bullo da shirye-shiryen karfafawar zamantakewar al’umma da nufin fitar da miliyoyin ‘yan Najeriya daga kangin talauci Wanda shine Babban ƙalubalenmu duk da haka wannan shine Hanyar da za’a iya ci gaba da karfafawa domin ci gaba da shirye-shiryen don cimma buri da manufofin Gwamnatin bamu da Rayuwa Mai tsada hakika ‘Yan Najeriya na sha’awar sakamako Kuma dole mu basu.

Ina kuma jinjina wa mai girma Gwamnanmu, Nasir Ahmad El-Rufai kan irin shirye-shiryen da yake aiwatarwa a cikin jihar Kaduna duk da kalubalen rashin tsaro. Ina roƙonmu da mu ci gaba da ba shi goyon baya kuma mu rinka tunawa da shi a cikin addu’o’inmu.

Ina kara jinjina ta musamman ga ‘yan uwa Kiristoci maza da mata a shiyyar kaduna ta tsakiya. Da suka kasance masu ban mamaki. Tare da ci gaba da goyon bayan ku zanyi aiki tukuru domin kara daukaka mazabar mu.

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya kiyaye mu ya kuma kai mu shekarar 2021. Da yardar Allah, za a samu manyan labarai na Alkhari a shekarar 2021 Mai Zuwa.

Barkanku da Kirsimeti!

Sanata Uba Sani (Kaduna ta Tsakiya)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button