Labarai

Sanata Uba Sani Ya kafa Tarihi A Majalisar Dattijan Nageriya.

Spread the love

Sanata Uba sani Bayan Ya Zama Sanata Mai wakiltar kaduna ta tsakiya har’ila yau Shine Sanata na farko da ya fara Samun wata babbar daraja a Majalisar Dattijan Nageriya a zuwan sa na farko Majalisar,
sanin kowa ne ba kasafai ake bawa sabon dan Majalisa shugabancin ko wanne irin kwamiti ba a zuwansa Majalisar na farko amma Sanata Uba sani sai gashi a zuwan sa na farko an nadashi shugabanci Kuma na babban Kwamiti Wanda ko tsofaffin gwamnoni da tsoffin sanatoci wa’yanda suka juma a Majalisar basu samu irin wannan damar ta Samun Shugabancin wagga babban Kwamitin ba,
wato kwamitin Bankuna Inshora da sauran harkokin da suka shafi kudi (Committee On Banking, Insurance And Other Financial Institutions) a tarihin Majalisar dattijan Nageriya wannan Kwamiti ba’a taba bawa wani dan Majalisa a zuwansa na farko Majalisar ba sai Sanata Uba Sani,
Bayan Haka Kuma Sanata Uba Sani Ya kasance memba Acikin kwamitoci har guda shida 6 a Majalisar Dattijan tarayyar Nageriyar.

KWAMATOCIN SUNE GASU KAMAR HAKA…

Sanata Uba Sani memba ne a kwamitin Sadarwa (Committee On Communications)

Memba ne a Kwamitin harkokin kasashen waje Da harkokin Gida Nageriya (Committee On Local And Foreign Debt)

Har’ila yau memba ne A Cikin Kwamitin kasuwanci da zuba jari (Committee On Trade And Investment)

Sanata Uba Sani memba ne a kwamitin Aiyuka da samar dasu (Committee On Labour And Productivity)

Memba ne a kwamitin yaki da rashawa da sauran laifukan da Suka shafi kudi (Committee On Anticorruption And Financial Crimes)

Sanata Uba Sani ya kasance banban memba a kwamitin Harkokin watsa labarai (Committee On Media & Publicity)

Bincike ya nuna cewa a Majalisar dattijan Nageriya ba’a bawa mutun shugabancin Kwamitin Bankuna da Inshora dole sai ya cancanta domin alfarma batayin aiki a wajen domin Abu ne da ake bukatar kwarewar aiki, hakika dole ne sai an tabbatar da cewa ka kasance mai Gaskiya da rikon Amana a tarihin rayuwarka, sai ka kasance Mai matukar zurfin ilimi Kan harkokin kudin tare da aiki tukuru kafin a baka wannan shugabancin, kasancewar Sanata Uba Sani Shine mafi cancanta a wagga mukami yasa aka bashi Kuma ko yanzu zamu iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu bisa ga bincikenmu..

Sanata Uba Sani yayi anfani da damar da Allah ya bashi a Majalisar domin samawa al’ummarsa cigaba masu tarin yawa, yayi aiki tukuru ba dare ba Rana wajen ganin Nageriya ta zamu manyan kudade domin inganta harkokin noma da kasuwanci da sauran harkokin cigaba musaman arewa wanda a yanzu Haka Sanatan shine Ya zama babban jagora wajen karbo Bilyoyin kudade daga kasashen duniya zuwa Nageriya…

Sanata Uba Sani dai Bayan kokarin Samar da kwaleji a Garin Giwa da Birnin gwari yanzu Haka Kuma sanatan Yana kokarin ganin samun yardar Majalisar Dattijan Nageriya Don canja tsarin Kwalejin kaduna ta tarayya (Kaduna Polytechnic) zuwa babbar jami’ar fasaha (University Of Technology) a duk kokarin sa na samawa kaduna Zaman lafiya kamar yadda masana suka ce ilimi shine Kan juya tunanin matasa daga daina aikata manyan laifukan…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button