Labarai

Sanata Uba Sani ya kawoma Nageriya Hikimar da za’a daina shigo da makamai ta barauniyar Hanya.

Kudirin Kwaskwarimar Dokar Makamai (2020) da mallam Uba Sani ya gabatar a majalisa ta tsallake karatu na biyu
A Kudirin daya gabatar Sanatan Mai wakiltar kaduna ta tsakiya a Majalisar dattijan Nageriya Uba sani ya bukaci a yi wa dokar Makamai kwaskwarima da sauran su, ta yadda za a kara tsaurara matakan hukunci a kan shigo da su ta barauniyar hanya, kuma masu mallakar su ba bisa ka’ida ba.

Wannan kudiri ya samu goyon Baya na sanata Biodun Olujimi da sauran sanatoci wanda Majalisa ta mika ta wajen kwamiti mai kula da harkokin kotuna, kare hakkin Yan kasa dan cigaba da aiki akanta.

Wannan kudirin doka na kwaskwarima akan dokan da ya shafi makamai shigo da su da mu’amala da su, yazo a lokacin da ya dace.

Kowa yasan halin da aka shiga na rashin tsaro a kasan nan shekaru da yawa da suka gabata. Wannan doka zai samar da hanya na hana mu’amala da muggan makamai da shigo da su ba bisa ka’ida ba.

Muna so ayi bincike a rubuta mana fa’idan wanann kudiri da anfanin shi ga al’umman Nigeria idan ya zama doka.

munason a rubuta article da hausa wanda zaiyi cikakken bayani akan fa’idan kudirin da hausa ko da turanci..Zamu dauki Article din da yafi muhimmanci muyi masu kyauta, kuma musa a buga a jaridun kasan nan In Sha Allah.

Wannan gasan kowa na iya shiga don muhimmancinta.

Sign:
Ibrahim Salisu Abubakar
Strategic Communication Officer
for: Chief Zonal Constituency Officer

10/02/2021

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button