Sanata Uba Sani Ya Lashe Lambar Yabon Shekara ta 2020 a Matsayin Sanata mafi Cika Alkawari.
Sanata Uba Sani Mai wakiltar kaduna ta tsakiya a Majalisar dattijan Nageriya ya lashe babbar lambar Yabo na Shekara Shekara ta Most Of promising Senator)
A jiya ne dai aka bayarda lamabar Yabon ga Sanatan A babban Hotel din Transcorp Hilton) dake babban Birnin tarayyar Nageriya Abuja.
A nasa bangaren sanata uba Sani ya rubuta a shafin sa na Twitter Yana Mai cewa hakika Babban abin Alfahari ne kasancewa an karramaka da “Kyautar Sanatan Shekara a bikin karrama jaruman Dimokiradiyya da aka yi a Abuja a ranar 14 ga watan Oktoba, 2020. Gwamnan jihar Kaduna Mai daraja, dan uwana, maigidana, abokina kuma abokin siyasa, Malam Nasir El-Rufa’i ya shima ya Samu halartar bikin domin bani goyon baya.
Kyautar za ta taimaka min domin wani sabon Salo aiki ga mutanena Zan kuma tabbatar da cewa batutuwan da suka shafi mutanen Najeriya sun sami kulawa ta gaggawa Baki daya.
Na sadaukar da wannan lambar yabo ga mutane masu daraja dake yankinmu na Sanatan Kaduna ta Tsakiya. Ba iya kawai wakilci suka bani ba, Har’ila yau suna ba ni cikakken goyon baya tun daga farkon tafiya ta majalisa.
Kalamai na sunyi kadan wajen furta kalmar godiya a gare su..
Sanata Uba Sani Sanatan kaduna ta tsakiya..