Sanata Uba sani ya tallafawa matan ‘yan Sandan da suka rasu da Naira Milyan biyu Kash..
Babban Mai taimakawa Sanata Uba sani Mai wakiltar kaduna ta tsakiya Bello El rufa’i Yace A safiyar yau, Mai Girma Sanata Uba Sani ya bayar da gudummawar zunzurutun kudi har Naira miliyan biyua wajen taron karfafawa na shekara-shekara na kungiyar matan jami’an ‘yan sanda. An bayar da wannan gudummawar ne a matsayin tallafi na jin kai ga matan da suka rasa mazajensu don hidimtawa Tarayyar Najeriya tare da kare al’umma.
Sanatan ya kuma yi alkawarin yin amfani da gidauniyar sa, ta Uba San Foundation) Domin cigaba da tallafawa ayyukan Kungiyar sannan kuma yayi alkawarin yin amfani da ofishin sa domin saukaka musu abubuwan nan gaba a matsayin wadanda zasu ci gajiyar Kudin Gwamnatin Tarayya na Musamman. Ya kuma jajantawa matan da suka rasa mazajen nasu yayin da yake yi musu jaje kan cewa sun rasa matansu ta hanyar da ta dace don kare hakkin al’umma.
Matan wadanda suka yi matukar farin ciki sun godewa Sanatan bisa irin gagarumar rawar da ya taka da kuma tausayin da yake nuna wa mambobinsu tare da basu tabbacin ci gaba da mara musu baya. Kungiyar Sun taya Sanatan murna kan dimbin nasarorin da ya samu tun bayan hawan sa mulki yayin da suka bayyana cewa ya zarce magabata wajen gudanar da ayyukan sa a majalisar.
Daga Babban Mataimakin Majalisar
Bello El-Rufai
6th Maris 2021