Labarai

Sanata uba Sani ya taya sabon Sarkin Zazzau murna ya kuma godema Gwamna El’rufa’i bisa zaben sarkin Daya dace da sarautar Zazzau

Spread the love

Sanata Uba Sani mai wakiltar kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattijan Nageriya ya taya sabon Sarkin Zazzau murnar samun Sarautar Zazzau Sanatan ya rubuta a shafin na Facebook yana mai cewa nima na shiga sahun mutane masu Albarka na masarautar Zazzau da miliyoyin ‘yan Najeriya da sauran masoya na duniya don taya murna ga sabon Sarkin Zazzau da aka nada, HRH Ahmed Nuhu Bamalli.
Muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da yasa muka ga wannan rana.
Zabar sabon sarkin daya kasance yake bukatar kyakkyawan dogon bincike mai zurfin gaske don neman wanda ya cancanci maye gurbin mai martaba Alhaji (Dr.) Shehu Idris, marigayi Sarkin Zazzau.

HRH Nuhu Bamalli ya hau gadon sarauta tare da kakkarfan zuriya; ingantaccen ilimi, wadatattun kwarewar da sanin darajar jama’a Haka nan kuma kwarewar sa ta diflomasiyya za ta kasance mai sauki ne a gareshi wajen tafiyar da al’amuran masarautar.

Ina yabawa mai girma Gwamnanmu, Malam Nasir El-Rufai da Sarakunan Zazzau da suka ba mu sabon Sarki wanda ya cancanci matsayin sananniyar Masarautarmu wanda bakinmu bazai isa ya iya gode maku ba Ina kira ga fadawan masarautar ta Zazzau da mutanen mu da su rungumi sabon Sarki su ba shi cikakken goyon baya domin Ta hanyar haɗa hannu ne kawai za mu iya ciyar da Masarautar tamu zuwa matsayi mafi tsayin girma.

Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya shiryar da kuma kare Mai Martaba Sarki yayin da ya fara mulkinsa wanda ya dauki alkawarin Jama’a

Sanata Uba Sani Sanatan Gundumar Kaduna ta Tsakiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button