Labarai

Sanata Uba Sani ya umarci Jami’ansa da cewa su hada rahoton bayarda kayan Agajin gaggawa ga wa’yanda Ambaliyar ruwa Ta shafa…

Spread the love

Sanata Mai wakiltar kaduna ta tsakiya a Majalisar dattijan Nageriya sanata uba sani Ya bayarda umarni ga Jami’ansa da cewa lallai su je su hada masa rahoton gaggawa domin bayarda tallafin na gaggawa ga Jama’ar da Ambaliyar ruwa ya shafa a wasu sassan yakin dayake wakiltar dayake cigaba da bayyana damuwarsa Kan aukuwar Al’amarin sanatan ya jajanta tare da addu’ar neman tsari daga Kan sake faruwar Al’amarin bayan haka Sanata Uba Sani, ya tattauna Da Gwamna Malam Nasir El-Rufai, da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna, ( Kaduna state Emergency Management Agency)
da Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Kaduna, (Kaduna State ministry of Environment) da Hukumar Bayarda da Agajin Gaggawa ta Nageriya (NEMA) a duk kokarin sanatan na Tabbatar da cewa an dau matakin gaggawa domin kawo agaji ga Mazauna Yankunan Da Ambaliyar ruwan Ya Shafa. Sanatan yace Zamu Kuma Yi Aiki Tare Da Hadin Kai Don Kawo Mafita Mai Dorewa Ga Matsalar Ambaliyar Ruwa A Wasu Sassan Yankin…

Har’ila yau Sanatan Kaduna Ta Tsakiya. Sanata Malam Uba Sani, Ya umarci Jami’an Mazabar sa na Kananan hukumomin da abin ya shafa da su hada masa rahotannin Tattaunawa akan Lamarin da ya faru domin sanin hanya da ka’idojin samarda kayan agajin gaggawa ga wa’yanda iftila’in ya faɗawa.

Idan baku manta ba dai a ranar talatane dai aka samu Ambaliyar ruwan a wasu sassa da sanatan ke wakilta a jihar ta kaduna…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button