Labarai
Sanata Uba Sani ya yi tir da Allah wadai kisan mutun 19 na Birnin Gwari da Kajuru.
Sanatan da ke wakiltar Kaduna Ta tsakiya a Majalisar Dattawa, Sanata Uba Sani ya yi tir da harin da ‘yan bindiga suka kai kauyukan Kananan hukumomin Birnin Gwari da Kajuru.
Sanatan ya bayyana rashin jin dadin sa bisa wannan hari yana mai mika ta’aziyyar sa ga ‘yan uwan wadanda aka rasa a wannan harin sannan kuma da jaddada kokarin gwamnati na ganin an kawo karshen hare-haren kauyuka a yankin wadanda basuji ba basu gani ba.
Bayan haka ya jinjina wa gwamnatin jihar Kaduna karkashin gwamna Nasir El-Rufai kan kokarin da take yi wajen ganin an kawo Karshen hare-haren ‘yan bindiga a jihar.
Sanatan ya kara da cewa za a aika da kayan tallafi na gaggawa ga wadanda wannan ibtila’i ya afka wa yana mai kira ga mutane da su kwantar da hankulan su.