Labarai

Sanata Uba Sani Zai Samawa manoma Mutun dubu 1,000 Naira Milyan bibiyu…

Spread the love

Sanata Uba Sani mai wakiltar kaduna ta tsakiya a majalisar Dattijan Nageriya tare da Hadin Kan Gidauniyarsa ta Uba Sani Foundation da Kwalejin Aikin Noma da Kimiyyar Dabbobi (College Of Agriculture and animal Science) dake Mando kaduna, sun hada karfi da karfe sun bawa matasa mutun dari 100 Horo Cikin mutun Dubu 1000 da Sanatan yayi alkawarin Daukar nauyinsu domin koya masu hanyoyin sanin dabarun dogaro da kai a Amfanoni da dama
a karon farko dai an koyawa matasan Kasuwancin kiwon Kifi da kiwon kaji a kwalejin ta Noma, haka zalika kuma Sanatan be tsaya anan ba harsai da ya tabbatar ya nemawa matasan lamuni daga babban bankin Nageriya CBN domin samun Makudan kudin da zasu fara aikin da aka koya masu kai tsaye…

Yanzu haka ana sa ran cewa ko wanne matashi guda daya da aka koyawa wannan dabaru zai samu lamunin kudi daga Naira Milyan biyu zuwa milyan uku bayan haka kuma sanata Uba Sani Na gaf da sake Dibar matasa mutun dari domin basu horo a wasu fannonin tare da basu Milyoyin kudade a duk kokarinsa na kawo karshen zaman kashe wanda ga matasan dayeke wakilta..

Sanata Uba sani ya sha alwashin cigaba da taimakon matasan kaduna dama matasan arewa baki daya tsawon zamansa a Majalisar Dattijan Nageriya kamar yadda ya tabbatar mana…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button