Siyasa
Sanata Ya Bukaci Shugaba Buhari Ya Kirkiri Barikin Soja A Yankin Shi.

Ahmed T. Adam Bagas
Sanata Mai wakiltar Gabashin Neja Muhammad Sani Musa 313, Ya yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, da Ya Kirkiri Barikin Soja ko Sansanonin Soji a Yan Kunan Kananan Hukumomin Shiroro, Rafi, Munya Da Suke Fama da Tashin Hankula.
Yan kunan da Suke Gabashin Jahar Ta Neja Suna Fama da Hare Haren Yan Bindiga Wanda a Cikin Makon da ya gabata ma Yan Ta’addan sunci Karensu Ba Babbaka Inda Suka Kashe mutane 15 Sukayi Garkuwa da mutane 8 Mutane sama da 2000 Suka Gudu sukabar Muhallinsu a Yankin.