Sanatoci Sun Bukaci Shugaba Buhari da ya daina Zuwa Kasar Waje Neman Lafiya.
Majalisar Dattawan Najeriya ta aika da gargadi ga fadar shugaban ƙasa kan kada Shugaba Buhari ya ci gaba da zuwa ƙkasar waje domin neman magani.
Sanata Ɗanjuma La’ah, wanda shi ke wakiltar Kaduna Ta Kudu, shi ne ya aika da gargadin inda ya ce asibitin fadar shugaban ƙasar zai gyaru ne kadai idan shugaban ya daina zuwa ƙasar waje domin neman magani.
Sanata Danjuma, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar da ke kula da hulda tsakanin bangarorin gwamnati, ya aika da gargadin ne ga babban sakataren fadar, Tijjani Umar, a lokacin da ya hallara gaban kwamitin domin kare kasafin kudin na 2021.
Jami’in fadar shugaban ƙasar ya gabatar da kasafin biliyan 19.7 a kasafin 2021, kuma a cikin kasafin, za a yi amfani da biliyan 1.3 wajen gyara asibitin fadar shugaban ƙasar.
Shin Masu Karatu Kuna ganin Hakan Zai Yiwu..???