Sanusi ya yi wa Tinubu karin haske kan aikin da yaje yi Nijar, ya ce ana kokarin dawo da zaman lafiya
Muhammadu Sanusi II, Sarkin Kano na 14, ya ce ya jajirce wajen ganin an dawo da zaman lafiya a Jamhuriyar Nijar.
Sanusi ya yi magana ne a ranar Laraba bayan ziyarar da ya kai Abdourahamane Tiani, jagoran juyin mulkin, a Yamai, babban birnin Nijar.
Tsohon sarkin ya bayyana cewa, duk da cewa jami’an gwamnati na sane da ziyarar da ya kai wa shugabannin da suka yi juyin mulkin, amma aikin na kan sa ne.
Ya ce ya yi wa shugaban kasa Bola Tinubu bayanin sakamakon taron, inda ya kara da cewa lamari ne da ke bukatar diflomasiyya.
“Ana ci gaba da shiga tsakani kuma za mu ci gaba da yin iya kokarinmu wajen hada bangarorin biyu domin inganta fahimtar juna,” in ji Sanusi.
“Wannan lokaci ne na diflomasiyya na jama’a, ba batun da za mu bar wa gwamnatoci ba. Duk ‘yan Najeriya da ‘yan Nijar na bukatar a hada kai don nemo hanyar da za ta taimaka wa Afirka, Nijar, Najeriya, da bil’adama.
“Ba gwamnati ce ta aiko ni ba. Jami’an gwamnati sun san cewa zan je amma ni kaina ne na yi amfani da abokan hulda na don isa wurin kuma zan ci gaba da yin iya kokarina. Ya zama wajibi na a matsayina na shugaba in yi hakan.”
Ziyarar Sanusi ta zo ne kwana guda bayan hukumomin sojan Nijar sun ki amincewa da tawagar samar da zaman lafiya ta kasashen yammacin Afirka (ECOWAS), Tarayyar Afirka (AU), da kuma Majalisar Dinkin Duniya (UN).
Kungiyar ta ECOWAS ta ce an kawo karshen tashe-tashen hankulan diflomasiyya ne biyo bayan wata sanarwa da hukumomin sojin Nijar suka yi da daddare wanda ke nuni da cewa ba su samu tarbar tawagar ba. Ita ma Victoria Nuland, mataimakiyar sakatariyar harkokin wajen Amurka, an hana mata izinin ganawa da Tiani ko hambararren shugaba Mohamed Bazoum. Maimakon haka, ta yi magana na tsawon sa’o’i biyu tare da wasu jami’an soja.