Labarai

Sarakunan Gargajiya Na Kabilar Inyamurai Sun Yabawa Buhari.

Spread the love

Sarakunan gargajiya daga Jihar Anambra sun Ziyarci Fadar Shugaban kasa a Yau Alhamis a Abuja sun nuna godiyarsu ga Shugaba Muhammadu Buhari saboda jajircewarsa ga ci gaban kasa gaba daya, musamman Kudu Maso Gabas.

Sanarwar da Femi Adesina, mai magana da yawun Shugaban Kasa ya Fitar ya ce, sarakunan, Wanda Yarima Arthur Eze ne ya jagorancesu a fadar Shugaban Kasa, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Farfesa Ibrahim Gambari ya karbi bakuncinsu a Gidan Gwamnati.

Mista Gambari, wanda ya yi godiya ga sarakunan gargajiyar saboda zuwansu, ya ce wannan karimcin zai karfafa wa Shugaban kasar damar yin abubuwa da yawa ga yankin da kuma kasa baki daya.

“Wannan wani lamari ne da zai karfafa wa Shugaban kasa guiwar yin abubuwa da yawa ga kasar, da kuma Kudu maso Gabas Inji Gambari.

Sarakunan sun lissafa ayyukan da gwamnatin Buhari ta bullo da su a yankinsu da suka hada da “gada ta biyu ta Neja, wacce gwamnatocin da suka gabata suka gabata suna daukarta a matsayin wani aiki mai wuya, amma yanzu ta zama gaskiya a karkashin kulawarku, Sai kuma Tagwayen Tituna da Suka hada Enugu zuwa Onitsha, Enugu zuwa Port Harcourt da sauransu.

Sun kuma yabawa Shugaban kasar saboda nada ‘ya’yan Igbo maza da mata a mukamai masu mahimmanci a cikin gwamnatinsa.

Sarakunan sarauta sun tabbatar da cewa a matsayinsu na Wakilan mutane, suna ganin ya zama wajibi gare su su “zo su nuna godiyarsu a madadin jama’ar yankinsu baki daya, kuma suna rokon Shugaban kasa da ya kara yin abubuwan alheri a yankin. “

Sarakunan sun hada da Eze Dr Nkeli Nzekwe, Igwe Chuba Mbakwe, Igwe Chijioke Nwankwo, Igwe Anthony Onwekwelu, da Igwe Chukwuma Bobo Orji.

Daga Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button