Sarakunan garganiya na karamar hukumar Bassa sun jinjinawa kokarin yaki da talauci da rashin aikin yi da gidauniyar Unity Foundation ke ci gaba da yi a jihar Plateau


Sarakunan garganiya na karamar hukumar Bassa sun jinjinawa kokarin yaki da talauci da rashin aikin yi da shaharrarriyar gidauniyar nan ta Unity Foundation ke ci gaba da yi a karamar hukumar Jos ta Arewa, Bassa da ma jihar Plateau baki daya, karkashin jagoranci hazikin matashin nan wato Alhaji Abubakar Salisu Yaro Mai Dankali.
Sarakunan sun yi wannan jinjina da yabawan ne yayin wata ziyarar ban girma da tawagar sarakunan na karamar hukumar Bassa suka kai masa ofishin kungiyar dake birnin Jos jihar Plateau.
Da yake jawabi a madadin tawagar sarakunan, Mai girma Sarkin Rukuba Atye Adamu ya bayyana cewa yanzu Alhaji Abubakar Salisu Yaro Mai Dankali ba kawai tallafi da koyar da mata da matasa sana’o’in dogaro da kai kawai yake yi ba, yana amfani da gidauniyarsa wajen taimaka wa wanzuwar hadin kai, ci gaba da zaman lafiya.
A nasa jawabin, Ugomo Aima Gurum ko kuma Sarkin Gurum kamar yadda ake fada ya bayyana cewa ziyarar da suka kai wa Alhaji Abubakar Salisu Yaro Mai Dankali, sun kai ta ne domin sake karfafa masa gwiwa:
Da yake mayar da jawabi, Shugaban gidauniyar Unity Foundation Alhaji Abubakar Salisu Yaro Mai Dankali, ya bayyana farin cikinsa da ziyarar, yana mai cewa wannan ba karamar karramawa bace tawagar Sarakuna tun daga Karamar hukumar Bassa su ziyarce shi.
Ya kara da cewa shi babban burinsa shine yaga al’umma sun zauna lafiya da junan su ba tare da nuna bambancin siyasa, kabila ci ko na addini ba:
Ya kuma yi albishir cewa nan ba da jimawa ba, gidauniyar ta Unity Foundation za ta kai ayyukan ta na koyar da sana’o’in dogaro da kai ga mata da ‘yan mata da matasa zuwa cikin Al’ummar Irigwe da Fulani, domin samar da hanyar da za su yi mu’amala da junan su tare jefar da duk wani gilli dake zukatan su da zimmar samu karin zaman lafiya da ci gaba.
Tashar Unity FM da TV ta ruwaito cewa sauran sarakunan da suka kasance daga cikin tawagar ziyarar sun hada da Mai Girma Sarkin Jebbu Miango Adama Gado, Mai Anguwan gundumar Miango zone, Shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore reshen jihar Plateau Alhaji Umaru Dakare, da shugabar kungiyar zaman lafiya ta matan Bassa wato Hajiya Rashida Usman Yahaya da sauran su.
Ita dai kungiyar Unity Foundation karkashin jagorancin Alhaji Abubakar Salisu Yaro Mai Dankali, kawo yanzu ta koyawa kimanin mata da matasa sama da #45,000. sana’o’in dogaro da kai daban daban a birnin Jos da kewaye.