Fashion

SARAUNIYAR BAKAKE TA DUNIYA “The Queen of Dark”

Daga Mutawakkil Gambo Doko

“Ms Gatwech Nyakim” wanda yanzu haka ta shahara a shafin yanar Gizo gizo na “Istagram” inda take da Mabiya (Followers) kusan Miliyan 1
.
Ms Nyakim Anyi Ittifakin ita tafi kowacce Bakar fata Baki a duniya, Wanda Asalin Iyayenta ‘yan kasar Sudan ta kudu ne (South Sudan), Ms Gatwech Nyakim Iyayenta sun haife ta a ranar 27 ga watan Janairu na shekara ta 1993 agarin Gambela na kasar Ethiopia
.
Bayan da Yakin Basasa ya barke akasar Sudan sai iyayenta sukayi Gudun Hijjira zuwa kasar Kenya inda daga bisani suka koma garin Gambela na kasar Ethiopia inda nan ne aka bawa iyayenta mafakar siyasa har suka haifi Ms Nyakim.


Daga bisani dai iyayen na Nyakim sun sakeyin gudun hijjira zuwa kasar Amerika alokacin Nyakim tana da shekara goma 14, Iyayenta sun zauna a Buffalo na birnin New York kafin daga bisani su Motsa zuwa Garin Minnesota na kasar ta Amerika.
Nyakim ta shiga Jami’ar “St Cloud state University) inda anan ne ta fara shahara alokacin da ta fito a Fostar wani Film Na Jigsaw 2017, Ms Nyakim taja hankalin Mutane da dama inda ta Rikayin Alfahari da Bakar fata da ALLAH (s.w.a) yayi mata, kuma ta kasance Mai Kalubalantar mutanen da suke Maida fatarsu zuwa Baka (skin Bleaching)
.
Menene ra’ayinku?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button