Labarai

Sarki Muhammadu Sanusi Na II, Ya Shawarci ’Yan Najeriya A Kan Su Yarda Ayi Masu Rigakafin Cutar Coronavirus

Spread the love

Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya kirayi al’ummar Najeriya da su karbi allurar rigakafin cutar Coronavirus da zarar an tanade ta a kasar.

Sanusi ya yi wannan kira ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da ya halarci wata laccar wayar da kai tare da Ma’aikatan Kiwon Lafiya na Najeriya mazauna ketare da aka gudanar a yanar gizo ta hanyar mahnajar fasahar sadarwar zamani ta Zoom.

Ya bayyana bukatar shugabanni su fadakar da jama’a game da muhimmacin rigakafin, wanda a cewarsa ta hanyar wayar da kai da yi wa al’umma karin haske ne kadai za a gaskata cutar.

“Ya kamata shugabanni su fito su shige gaba wajen jagorantar al’umma ta hanyar karbar allurar rigakafin cutar a bainar jama’a wanda ta hakan ne kadai za a yarda da gaskiyar cutar.”

“Mutane ba za su amince da rigakafin ba matuka shugabanni suka juya mata baya, saboda haka ya kamata shugabanni su karbi rigakafin sannan iyaye su nuna ’ya’yansu muhimmancin karbar rigakafin,” inji shi.

Ya kuma yi kira a kan koda yaushe mutane su ci gaba da kiyaye ka’idodin kariya na dakile yaduwar cutar ta Coronavirus sannan kuma su karbi rigakafinta da zarar an tanade ta a kasar nan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button