Ilimi

Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar Na III, ya yabawa Gwamna Tambuwal kan Ilmi a Jihar.

Spread the love

Kwamitin inganta Ilmi na jihar Sokoto da Mai Alfarma Sarkin Musulmu Dr. Sa’ad Abubakar ke jagoranta ya karbi kudin da ake cirewa Ma’aikata a matsayin tallafin inganta Ilmi a Sokoto, har na Naira Biliyan 1 da Miliyan 138 daga watan juni na shekara ta 2017 zuwa 20 ga watan Satumban 2020 inda a cikin lokacin aka kashe Naira Miliyan dari 833 inda ake da Naira miliyan 305 a asusun yanzu haka.

Cikin ayukkan da akayi an gina makarantu guda 13 masu azuzuwa 6 a yankuna 3 na dan majalisar tarayya.

Hakama an gina makarantun boko da tsangaya guda 100 a duk fadin jihar Inji Shi.

Mai Alfarmu Sarkin Musulmi Dr. Muhammad Saad Abubakar na III, ne ya sheda haka a lokacin da yake wa Gwamna Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal bayani akan ayukkan kwamitin a fadar gwamnati a yau Laraba.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button