Uncategorized

Satar Garin Tuwo A Kano Ta Tilastawa Masu Nika Bada Katin Sheda

Spread the love

Wata sabuwar Sata Ta bullo A wasu sassa na Bangaren kano ta Daukewa jama’a gari idan sunkai nika wajen masu inji.

Wannan matsalar dai kwana kwanan Nan ta shigo garin kano din, inda idan mutum ya kai nika inji sai dai yazo ya tarda wani ya rigashi dauka.

Wannan dalilin yasa Masu Injina a kano suka bullo da wata sabuwar hanya domin magance irin wadan nan matsalolin na satar, Sunbuga katin shaida Wanda idan kazo daukar nika saika nunashi sannan ka dauka.

Har wa yau, wasu na alaƙanta al’amarin da irin matsin rayuwar da jama’a suka samu kansu a ciki saboda tashin gwauron zabi da farashin kayan masarufi ya yi sakamakon karin kudin man fetur da wutar lantarki da gwamnatin Najeriya ta yi.

Ana tunanin wannan matsalar tana afkuwa ne a dalilin tashin Gwauron zabi da kayan abinci yayi a wannan lokacin da muke ciki.

Kayan masarufi yayi tsada hakan yake jefa wasu izuwa wannan Halin na daukarma wasu gari a wajen masu nika. Daga Ibrahim Dau Mutuwa Dole

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button