Satar Makarantar Zamfara: Kusan ‘yan mata 550 sun bata.
Daga cikin dalibai 600 na makarantar sakandaren ‘yan mata ta gwamnati, dake Jangebe, a karamar hukumar Talata Mafara ta jihar Zamfara, an bar kimanin 50 a baya, …
Daga cikin dalibai 600 na makarantar sakandaren ’yan mata ta gwamnati, da ke Jangebe, a karamar Hukumar Talata Mafara, ta Jihar Zamfara, an bar kimanin 50, kamar yadda wani malamin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Jaridar Aminiya.
Wasu ‘yan bindiga sun kutsa kai cikin makarantar da safiyar ranar Juma’a, inda suka yi awon gaba da dalibai da dama.
Malamin ya ce iyayen daliban, wadanda suka tsere daga satar, sun zo ne tun da misalin karfe 5 na asuba don kwashe ‘ya’yansu mata, ya kara da cewa wasu iyayen yan matan da aka sace suna zubewa a harabar makarantar.
“Da farko, hukumomin makarantar sun hana su tafiya tare da sauran daliban amma suka kara fusata suka fara sauke kofofi da tagogin gine-ginen da ke cikin makarantar kuma dole ne hukumar makarantar ta mika wuya ga bukatunsu.
“Lokacin da :yan bindigan suka yi wa makarantar kawanya, sai da suka far wa sojojin da ke yankin kafin su samu shiga makarantar.
“Wasu mutane sun gaya mana cewa sun ajiye motoci a gefen makarantar.
“Jami’an tsaro da kungiyoyin sa kai na yankin suna bin sawun ‘yan bindigar kuma wasu da dama daga cikin mazauna yankin sun ba da kansu don shiga cikin binciken,” in ji shi.
Sai dai Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce ba a san adadin daliban da aka sace daga makarantar ba.
Da yake magana, kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sulaiman Tunau Anka, ya ce har yanzu ba a gano takamaiman adadin daliban da aka sace ba.
“Har yanzu ba mu tabbatar da ainihin adadin daliban da aka sace ba.
“Jami’an tsaro sun fara farautar wadanda suka aikata laifin.”
“Sun tafi makarantar da motoci. Wasu daga cikin ‘yan matan sun yi tattaki. Muna kan halin da ake ciki yanzu saboda duk wani tuntuba ana kokarin ganin an ceto ‘yan matan makarantar da aka sace, ”inji shi
Satar ta faru ne ‘yan sa’o’i bayan da gwamnatin jihar ta ce wasu tubabbun’ yan bindiga sun mika makamansu.
Gwamna Bello Matawalle na Zamfara yana ci gaba da tattaunawa da ‘yan bindiga don samun zaman lafiya.