Satar yara tazo karshe a jihar kano
Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya kaddamar da kwamitin zartar da rahoton hanyoyin shawo kam matsalar sace yara da akeyi wanda a kwamakin baya aka kama wasu yan kudu wanda suka dade suna wannan mummunan aiki. Gwamnatin jiha tare da hukumar yansanda sun yi nasarar samo wasu daga cikin yaran wanda aka maida su hannun iyayen su.
Sakamakon wannan ne Gwamna Ganduje ya ga dacewar kafa wannan kwamitin domin ganin cewa irin wannan bata sake faruwa ba a Kano.
Kwamitin na karkashin Jagorancin Mai Shariah Wada Umar Rano, kuma ya na da membobi da suka hada da wakilin hukumar yan sanda, da na jami’an tsaro na farin kaya, da na shige da fice, da hukumar yaki da safaran mutane musamman yara da kungjyar malamai wato Council of Ulama da kuma Shugaban Kungjyar Kiristoci reshen jihar Kano da sauran su.
Salihu Tanko Yakasai
Special Adviser Media
Government House Kano
July 4, 2020.