Labarai

Sau biyu Sanata Rabi’u kwankwaso Yana tura Dansa kasar India Karatu.

Spread the love

Malam Shaharani mahaifi ne na daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar Tsarin tallafin Karatun Kwankwasiyya. Mahaifin (Mashahud) ya sami tallafin sau biyu daga gwamnatin Sanata Rabi’u Kwankwaso domin samun digiri na farko da Msc na gidauniyar Kwankwasiyya Development Foundation, duk Zuwa kasar Indiya.

Yayin da yake kuka da godiya ga Sanata Kwankwaso a jiya a madadin sauran iyayen da suka ci gajiyar wannan shirin, yayin wani taron baje kolin kwanaki 3 na Daliban da gidauniyar ta dauki nauyin karatunsu a tsarin Kwankwasiyya, ya ba da labarin yadda ya taka a Kafa daga gidansa zuwa gidan gwamnatin jihar Kano da Naira 10 kacal a aljihunsa domin zuwa ya gabatar da takardun shaidar dansa, bayan ya ji a gidan Rediyo, sanarwar tallan Ilimi zuwa kasashen waje da gwamnatin Kwankwaso ta yi ga wa’yanda suka kammala karatun Sakandaren Jihar Kano Kuma wanda ya kammala da maki 9. Wato, a shekara ta 2012.

An yi sa’a, an tura Dansa zuwa Jami’ar Sam Hagginbattom Dake kasar Indiya domin karatun sa na farko inda ya samu digiri na 1 a Fannin magani. Bayan dawowarsa, Har’ila yau Gidauniyar ci gaban Kwankwasiyya karkashin inuwar sanata Kwankwaso ta sake daukar nauyinsa zuwa Jami’ar Sharda da ke Indiya inda ya yi karantunsa na Msc.

Ya ba da labarin yadda duk wannan ya faru ba tare da alaƙa da Kwankwasiyya ba ko Kwankwasiyya Development Foundation ba.

Ku Zo mu canza rayukanmu, mu zama Kamar Kwankwaso na wannan lokacinmu.

Daga, Ibrahim Adam Fassara Jaridar Mikiya…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button