Labarai
Saudi Arabiya ta bayar da tallafin guraben karatu ga d Yan Najeriyar 424
Masarautar Saudi Arabiya ta bai wa daliban Afirka guraben karatu har mutun 6,597 a kowace shekara don yin karatu a fannoni daban-daban a Jami’o’in Saudiyya.
Wata sanarwa da aka aika wa HAJJ REPORTERS ta Ofishin Jakadancin Masarautar Saudiyya a Najeriya ta ce “daga cikin guraben karatu 6,597, an warewa Nageriya 424 a duk shekara”.
Sanarwar ta kara ba yan takarar masu sha’awar neman hanyoyin da yanayin da za su nema don neman karin bayani daga Ma’aikatar Harkokin Waje ko Ma’aikatar Ilimi na Kasashensu.