Labarai

Saudi Tace Babu Mai dauke da CoronaVirus a mahajjata mutun milyan Biyar 5m.

Spread the love

Saudi Arabiya ta karbi mahajjatan Umrah miliyan 5 da masu yin ibada tun lokacin da aka dawo da ibada, in ji Ministan Hajji da Umrah Dr. Mohammed Saleh Benten.

Ya ce babu wani rahoton cutar COVID-19 da aka ruwaito tsakanin mahajjata da masu ibada. Wannan bayanin ya fito ne yayin ganawa da Gwamnan Makkah Yarima Khaled Al-Faisal a Jeddah a ranar Laraba.

Saudi Arabia ta dakatar da Umrah a watan Maris kuma ta rage aikin hajji a watan Yuli ta hanyar bawa mahajjata dubu daya kawai, duk a matsayin martani ga annobar COVID-19. Masarautar ta dawo kan hanya bayan dokar kulle da ta gabata yayin bin ka’idojin lafiya.

A ranar 22 ga watan Satumba, masarautar ta sanar da dawo da aikin Umrah a hankali a matakai hudu.

Ofisoshin yawon bude ido a kasashen waje suna bin kwantaraginsu da Ma’aikatar Aikin Hajji da Umrah domin mahajjata su zo su yi aikin Umrah.

A kashin farko, wanda ya dauki kwanaki 14, an karbi mahajjata 84,000 – mutane 6,000 a kowace rana. Kimanin mahajjata 210,000 ne suka yi aikin Umrah a kashi na biyu.

Kashi na uku, wanda aka fara a ranar 1 ga Nuwamba, ya ba mahajjata daga kasashen waje damar yin aikim tare da mazauna Masarautar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button